Below is the text of the page https://www.voahausa.com/a/3315108.html stored 2016-05-26 by archive.org.ua. The original page over time could change. View as original html

Donald Trump Yace Nasarar Da Ya Samu Gagaruma Ce

Accessibility links Koma Ga Cikakken Labari [#content] Koma Ga Babbar Kofa Koma Ga Bincike Search Search Harsuna Na Baya Na Gaba 0 Labari da Dumi-Duminsa Na Baya Na Gaba 0 Kai Tsaye Sauran Duniya Donald Trump Yace Nasarar Da Ya Samu Gagaruma Ce Mayu 04, 2016 Abubakar Jinaidu Rarraba Nuna wa mutane akan Facebook Nuna wa mutane akan Twitter Nuna wa mutane akan Google+ Tura Ga Aboki ta Email See comments Donald Trump bukaci hadin kan 'ya'yan jam’iyyar Republican WASHINGTON, DC — Shugaban jam’iyyar Republican na Amurka yace yana gani n cewa yanzu ta tabatta da cewa kusan Donald Trump ne wanda jam’iyyar zata tsaida a matsayin dan takarar shugaban kasa bayan da ya sami nasara a zaben fidda gwanin da aka yi jiya a jihar Indiana. Trump ya sami kuri’u kashi 53 cikin dari, Sanata Ted Cruz kuma ya zo na biyu da kashi 37, da ga nan sai gwamnan jihar Ohio John Kasich, wanda ya sami kashi 7 cikin dari na kuri'un da aka jefa. Bayan kayen da ya sha a zaben da aka yi jiya a jihar Indiana a kokarin da ya ke yi don ganin ya takawa Trump burki wajen samun wakilan da jam’iyyar Republican ke bukata don fidda dan takara, Cruz ya janye daga takarar. Ya fadawa magoya bayansa cewa babu damar ya cigaba da gwagwarmayar neman takara tunda masu zabe sun zabi wani. Trump ya ce nasarar da ya samu gagaruma ce. Ya kuma yabawa Cruz, yana mai cewa Cruz din da sauran wadan da suka kara da shi sunyi kokari. Trump kuma yai kiran hadin kan jam’iyya. Shima shugaban jam'iyyar ta republican, Reince Preibus, irin sakon da ya aikawa 'yan jam'iyyar ke nan, inda ya neme su hada kai don samun galaba akan Hilary Clinton. A jam’iyyar Democrat kuma, Sanata Bernie Sanders ya doke abokiyar takararsa Hilary Clinton a zaben na jihar Indiana, inda ya sami kashi 53 cikin dari na kuri'un da aka jefa jiya. Amma duk da nasarar da ya samu a jiyan, har yanzu akwai tazara sosai tsakanisa da Clinton, yana neman gagarumar nasara a zaben da za a yi a sauran jihohin da suka rage kafin ya iya sha gabanta. Related Shugaba Obama yace tun ranar da ya kama mulki ya kuduri aniyar kashe Osama Bin Laden Trump ne ke kan gaba a jihar Indiana a zaben fidda gwani na Republican 'Yan Shi'a sun janye zanga zangarsu a Bagdaza 'Yan adawan Venezuela na cigaba da kokarin tsige shugaban kasar Amurka da Rasha su daidaita lamura tsakaninsu a yankin Baltics -Admiral Richardson Jami'an Kenya sun kama mai ginin da ya rushe ya hallaka mutane Direbobin tankokin dakon man fetur na barazanar shiga yajin aiki You might like also Sauran Duniya Isra’ila Ta Kara Yawan Ministocin A Gwamnatin Hadin Guiwa Sauran Duniya Kasashen Masu Amfani Da Kudin Euro Sun Cimma Gagarumar Nasara Sauran Duniya Haibatullah Akhunzada Shine Shugaban Taliban Sauran Duniya Masu Zanga-Zanga Sun Fusata Da Donald Trump A Jihar New Mexico Najeriya Da Mai Gwamnan Ekiti Ya Dogara Akan Hana Fulani Kiwo Afirka Ba Zasuyi Kasa A Guiwa Ba Wajen Tabbatar Da Tsaron Show comments Loading comments... Back to top Biyo Mu Shirye-Shirye Shirin Safe Shirin Hantsi Shirin Rana Shirin Dare Yau Da Gobe Taskar VOA VOA Hausa Najeriya Afirka Sauran Duniya Kiwon Lafiya Labarai a Takaice Rumbun Hotuna VOA60 Afirka VOA60 Duniya Bidiyo News in English Musamman Rahoto Sauyin Yanayi Yana Yin Mummunar Illa Ga Muhalli A Kasashenmu USA Votes 2016 Matsalolin Arewacin Najeriya Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi Taron Majalisar Dinkin Duniya YALI Fellowship Zaben Najeriya 2015 Shugaba Buhari Zai Ziyarci Shugaba Obama Labarin Soja Cutar Ebola Nelson Mandela 1918-2013 VOA Africa Afaan Oromoo Amharic English Kinyarwanda Kirundi Ndebele Portuguese Shona Somali Swahili Tigrigna Zimbabwe XS SM MD LG