Najeriya
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu Ya Kafa Kwamiti Akan Ebola
Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi, na biyu ya kafa wani kwamitin wayarwa da jama’ar masarautar Kano kai dangane da cutar Ebola.
Abubakar Jinaidu
An Sabunta Da Karfe 15.08.2014 21:41
WASHINGTON, DC— Mai martaba sarkin Kano , Alhaji Muhammad Sanusi, na biyu ya kafa wani kwamitin wayarwa da jama’ar masarautar Kano kai dangane da cutar Ebola.
Jami’in yarda labarai na kwamitin Alhaji Tijani Ado, yace babban abunda sarki ya umarce su shine, na wayar da kan alumar masarautar masamman wadanda ke karkara.
Da kuma tuntunbar Hakimai da dagatai da duk shuwagabanin aluma ta kowace bangare domin tabbatar da ganin cewa jama’a sun illimatu dagane da cutar ta Ebola.
Kwamiti kan ebola - 1'15"
- Kwandon Shirye-shirye na
- Sauko Da Sauti