This version of the page http://www.voahausa.com/a/3408982.html (0.0.0.0) stored by archive.org.ua. It represents a snapshot of the page as of 2016-07-17. The original page over time could change.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Zata Kara Bincike Kan Hillary Clinton

Accessibility links

  • Koma Ga Cikakken Labari
  • Koma Ga Babbar Kofa
  • Koma Ga Bincike
Harsuna
Sauran Duniya

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Zata Kara Bincike Kan Hillary Clinton


John-Kirby mai magana da yawu Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka

  • Nuna wa mutane akan Facebook
  • Nuna wa mutane akan Twitter
  • Nuna wa mutane akan Google+
  • Tura Ga Aboki ta Email

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace zata sake bincike na cikin gida ko mai neman takaran shugaban kasa a karkashin tutar jamiyyar Democrat Hilary Clinton ita da wasu hadiman ta sunyi anfani da sahihan bayanai lokacin da take sakatariyar harkokin wajen Amurka karkashin Shugaba Barrack Obama.

Zamu yi bakin kokarin mu muga cewa mun gudanar da binciken kan lokaci, amma kuma ba zamu sa wani kayyadadden lokaci ba, inji mai Magana da yawun ma'aikatar na cikin gida John Kirby.

Yace wannan bincike na cikin gida zai iya ci gaba a halin yanzu, musammam da yake yanzu ma'aikatar shari'a ta kammala nata ba tare da tuhumar Clinton ba.

Wannan dai yazo ne rana guda bayan da Atoni Janar ta kasa Loretta Lynch ta amince da duk shawarwarin da FBI ta bayar na cewa ba za'a tuhumi Clinton ba da aikata ko wane irin laifin assha game da wannan lamari.

Sai dai ‘yan jamiyyar Republican ciki ko harda abokin karawar ta Donald Trump sun koka akan wannan mataki da aka dauka game da Hilary Clinton game da batun email, yana cewa akwai coge, yace irin tasirin da take dashi a harkokin siyasar kasa ya agaza mata ta tsallake hukunci akan aikata ayyukan assha game da anfani da email din da tayi lokacin da ta rike mukami.

Sai dai hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI, ta kare matakin da ta dauka na cewa ba zata tuhumi Hilary Clinton da wani laifin aikata aikin assha ba, na anfani da bayanan email, lokacin da take sakatariyar harkokin wajen Amurka,duk ko da yake masu bincike sunce akwai sakaci wajen anfani da email dinta data yi.

Related

  • Babu Kwakwarar Shaida da Zata Sa A Gurfanar da Hillary Clinton A Kotu - FBI

  • Wakilan Jam’iyar Republican A Majalisar Amurka Sun Fusata Akan Batun Hilary Clinton

You might like also

  • Afirka

    Ba Tabbacin Kasashen Afirka Za Ta Yi Batun Sudan Ta Kudu a Taronsu Na 27

  • Afirka

    Hukumar Zaben Ghana Tace Ba Gaskiya Ace Ba Su Shiryawa Zabe Ba

  • Sauran Duniya

    Trump Ya Bayyana a Karon Farko Tare Da Pence a Matsayin Mataimakinsa

  • Sauran Duniya

    Na'urar Soji Mai Gano Jiragen Karkashin Teku Zata Sa Halittun Ruwa a Hatsari

  • Sauran Duniya

    Dan Adawa Ya Bukaci a Sawa Cambodia Ido Bayan Kashe Mai Fashin Baki

  • Afirka

    Kungiyar Amnesty Ta Zargi Sudan Ta Kudu Da Hana Jama'a Guduwa

Show comments

Back to top
XS
SM
MD
LG