Shugaban ‘yan adawa na jamiyyar ZAMBIAN FOR EMPOWERMENT AND DEVELOPMENT PARTY (ZED) ya amince zai mara wa shugaba Edgar Lungu na jamiyyar Patriotic front baya, a zaben da za’a yi a ranar 11 ga watan Agusta na wannan shekarar.
Shi dai wannan shiri an zo karshensa ne ran 30 ga watan Yunin wannan shekarar
Wasan da aka shirya din ya fara ne da misalign karfe 9 na daren jiya Laraba a agogon kasar, inda aka cika wani gidan wasa don yin wasannin sallah.
Izuwa yanzu akwai mutane ukku dake kwadayin darewa kan kujerar shugabancin
Wasu rahotannin kwamitin dake kula da sha'anin kudi a majalisar dokokin kasar Nijar ya gano cewa an fitar da wasu kudade kimanin miliyan dari bakwai na sefa ko kuma kwatankwacin nera miliyan dari uku da ishirin da biyar daga asusun majalisar ba bisa ka'ida ba.
Isa Ciroma Bakari, mai magana da yawun gwamnatin Kamaru yace 'yan kungiyar Boko Haram da yawansu ya kai dari sun kaiwa kauyen Homeka dake bakin iyaka da Najeriya hari wurin da ofishin dakarun hadin gwuiwa yake.
A yayinda daruruwan lauyoyin Kenya suka yi jerin gwano domin nuna rashin amincewar su ga zargin cewa yan sanda sun harbe wani abokin aikin su da wasu mutane biyu.
A yayinda ta ke yanke wannan hukunci, mai shari’a Thokozile Masipe tayi misali da takaicin da Pistorius ya nuna a lokacinda yake wa’adin hukuncin farko
Shugaban Uganda, Yuweri Museveni ya ce kasar za ta sake yin dubi kan batun shirinta na janye dakarunta daga Somalia, idan har shirin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika na AU ya daidaita.
Firayim Ministan Israila Benjamin Natanyahu ya kai ziyara kasashen Afirka hudu dake gabashin nahiyar, to ko wannan ziyarar zata yi tasiri tare da alfanu ga kasashen da ita Israila din?
Firayim Minista Isra’ila Benjamin Netenyahu yana kasar Uganda, a wata ziyarar da ba kasafai akan yita ba zuwa kasashen yankin saharar Afirka, ziyarar da ya fara don tunawa da wani ceton wadansu da aka taba garkuwa da su a shekarar 1976.
Kotun kolin kasar Austria ta yanke hukunci a yau Juma’a na soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Mayu, bayan da sakamakon kalubalantar zaben da jam’iyar Freedom ta shigar wanda dan takararta Norbert Hofer ya fadi zabe da karamar rata.
An kashe a kalla mutane shida lokacin da wani dan bindiga ya bude wuta kan wadansu motocin safa biyu a Kenya kusa da kan iyakar Somalia yau Juma’a.
Wasu ‘yanjami’ar birnin Nairobi dake kasar Kenya sun kwashe shekaru biyu domin samar da wata naura da zata inganta rayuwar mata masu juna biyu da kuma lafiyar jarirai.
A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani harin ta’addanci
A Africa ta Kudu ana sa ran shugaban kasar Jacob Zuma zai biya rabin dala milyan daya, ga asusun gwamnatn kasar, bayan kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin cewa tilas shugaban ya biya wani kaso na dala milyan 16 kudaden gwamnati da aka yi amfani da su wajen sake gyara gidan Zuma na kansa a garin da ake kira Nkandla.
An kashe ‘yan yakin sa kai goma sha takwas da sojojin gwamnati biyar da kuma wani farar hula a fafatawar da aka yi
Haka kuma kotun ta bukaci baitulmalin kasar ya tantance nawa shugaba Zuma zai biya domin gyaran gidan nasa
Kasar Nijar ta zama tamkar wata babbar matattara da masu safarar miyagun kwayoyi suke yin anfani da ita suna ketarawa kasashen Larabawa da nahiyar Turai abun da gwamnatin yanzu tace zata yaka kain da nain.
Biyo bayan harsashen da masana yanayi suka yi cewa daminar bana a jamhuriyar Nijar zata zo da ambaliyar ruwa a wasu wurare dalili ke nan da gwamnatin kasar ta yi shiri na musamman kafin lokacin.
Kasar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ta kaddamar da wani shirin yaki da cutar shawara ko kuma yellow fever, inda za a yiwa mutane miliyan 11.6 allurar rigakafin cutar nan da wata mai zuwa.
Uwargidan shugaban Amurka, Michelle Obama, na ziyara a kasar Morocco, a wani mataki na fadada samar da ilimi ga ‘ya’ya mata a duk fadin duniya.
A Ghana speto janar na 'yan sandan kasar, John Kudalor, yace jami'ai zasu kasance "yan ba ruwana," a babban zaben a ksar da za'a yi cikin watan Nuwamban bana.
Amurka tasa takunkumi ga babban jamiin rundunar ‘yan sandan birnin Kinshasa na Jamhuriya Demokaradiyyar Congo, sakamakon tada hankali da kuma kashe wasu fararen hula.
Farmakin da kawancen sojojin kasashen tafkin Chadi ke kaiwa kan 'yan Boko Haram a dajin Sambisa ya tilasta ma 'yan kungiyar arcewa zuwa kauyukan dake arewacin Borno kan iyaka da kasashen Nijar da Chadi
A Somalia, sojojin kasar sun kashe mayakan sakai na al-Shabab, suka kuma gano makamai da albarusai, a wani matakin soja da suka dauka jiya Laraba a tsakiyar kasar, kamar yadda jami'an gwamnati da mazauna yankin suka bayyana.
Eriteria ta fadawa kungiyar kare hakkin jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya cewa kasar Ethiopia na shirin kaddamar da yaki gadan gadan akan yankin ta.
Wannan wani bangare na ci gaban binciken Sojojin da ake zargi da yunkurin kifarda gwamnatin kasar ta Nijar
Wani dan rajin kare hakkin bil adama dake jihar Gbaduwe ta kasar Sudan ta Kudu, yace tashe-tashen hankula a gundumar Yambio sai karuwa yake yi.
Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, ta yankewa tsohon mataimakin shugaban kasar Congo, Jean- Pierre Bemba hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 18, bayan da ta same shi da laifin ingiza gudanar da ayyukan fyade da kisa a Jamhuriyar tsakiyar Afrika da ke makwabtaka da su.
Majalisar Dinkin Duniya za ta tura karin dakaru a cigaba da tallafawa yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a Mali, a cewar Majalisar, yayin da ake bikin cika shekara guda da shiga tsakanin da ta yi a rikicin kasar da ke Yammacin Afrika.
Wasu 'yansandan Kenya biyar sun mutu a wani harin da ake kyautata zaton 'yan bindigan al-Shabab masu tsattsauran ra'ayi ne su ka kai, kan wata tawagar motocin 'yansanda da ke tafiya a arewa maso gabashin kasar, a cewar wani jami'in yankin.
Satar jarabawar kammala karatun ilimin sakandare a jamhuriyar Nijar na neman zama ruwan dare gama gari domin ko 'yan watannin da suka gabata sai da satar jarabawar masu koyan aikin jinya ta jawo cecekuce domin samun hannun wasu manya a lamarin
Yau kasashen duniya ke bikin tunawa da ranar yaki da gusowar hamada
A jiya Alhamis ne kasar Eritrea tace ta kashe sojojin Habasha sama da 200, ta kuma raunata sama da 300
Dan takarar mataimakin shugaban kasar Zambia a jam'iyyar adawa ta United Party For National Development UNDP,Geoffrey Mwamba ya kalubalanci gwamnatin shugaba Edger Lungu data kama shi idan har gwamnatin ta kammala bincike kuma ta gano cewa yayi anfani da takardun jabu ne wajen tsayawa takarar a zaben da kasar zata gudanar a cikin watan Agusta.
Mahunkutar kasar Habasha sunyi watsi da wani rahoto mai shafi 61, da kungiyar nan mai kare hakkin bil adama da ake kira HUMAN RIGHT WATCH ta bada bayanin kashe mutane sama da 400 cikin watanni 7 da suka gabata a kasar ta Habasha,
Wani babban jamiin asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, yace ba za a rasa yara da yawan su yakai 5,000 ba a Somalia wadanda suke cikin sojojin al-Shabab.
'Yan kasashen Afirka da yawa ne suke ratsawa ta hamada zuwa Algeria da Libya da nufin shiga nahiyar turai saboda kuncin rayuwa da suke fama dashi a nasu kasashen kuma sau tari mutane na mutuwa a hamada ko kuma su nutse a tekun baharum
Majalissar dokokin kasar Somaliya ta amince da sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar jiya Laraba wanda zai yarda majalissar ta cigaba da ayyukanta ko da shugabannin kasar sun kasa gudanar da zaben kasar wanda ake shirin yi.
Akwai fargaban cewa mutane da yawa sun mutu bayan da wani fada ya barke jiya Laraba, tsakanin dakarun gwamnati da mayakan wata kungiyar ‘yan bindiga da ba sannaniya ba a garin Raja dake sabuwar jihar Lol dake kasar Sudan ta Kudu.
Wata kungiyar kare hakkokin bil’adama ta ce dakarun tsaron kasar Habasha sun kashe mutane fiye 400 tun cikin watan Nuwambar bara a wani mataki da suka dauka akan wasu masu zanga-zanga a yankin Oromia na kasar.
A yayin da mayakan kungiyar Boko Haram suka bude kafar watsa labarai ta tashar FM mai karamin zango a jihar Arewa Mai Nisa dake jamhuriyar Kamaru.
Tun ba yau ba shugaban kasar Nijar yace mutane daga wasu kasashen Afirka sun mayar da kasarsa wata zangon ratsawa ta zuwa nahiyar Turai lamarin da kan sa wasunsu su rasa rayukansu ko a cikin hamada ko kuma cikin tekun baharum