This version of the page http://www.voahausa.com/a/3357261.html (0.0.0.0) stored by archive.org.ua. It represents a snapshot of the page as of 2016-06-12. The original page over time could change.
Yawan Mutanen Dake Rasa Rayukan Su A Fallujah Na Karuwa

Accessibility links

  • Koma Ga Cikakken Labari
  • Koma Ga Babbar Kofa
  • Koma Ga Bincike
Harsuna
Sauran Duniya

Yawan Mutanen Dake Rasa Rayukan Su A Fallujah Na Karuwa


Sojojin Iraqi

  • Nuna wa mutane akan Facebook
  • Nuna wa mutane akan Twitter
  • Nuna wa mutane akan Google+
  • Tura Ga Aboki ta Email

Dakarun Iraki sun kaddamar da wani farmaki da niyyar kwato garin

Yawan mutane farar hular dake rasa rayukkansu a rikicin birnin Falluja na kasar Iraq na karuwa sosai yayinda yakin kwato birnin wanda ke hannun ‘yan ISIS ke kara tsananta.

“Wani bala’i ne yake faruwa a birnin yanzu haka. Rikicin ya rutsa da iyalai masu yawa kuma babu mafita," a cewar Jan Egeland (YAAN AY-guh-lan) na hukumar kula da ‘yan gudun hijirar kasar Norway.

Dakarun Iraki sun kaddamar da wani farmaki da niyyar kwato garin ne.

Akalla akwai yara 20,000 da rikicin ya ruttsa da su a cikin birnin, a cewar wata sanarwa da hukumar tallafawa asusun yara na Majalisar dinkin duniya, da ake kira UNICEF ta fidda. Hukumar ta yi kira ga duk bangarorin da ke fafatawa da su tabbata sun kare rayukan yaran, wadanda ke cikin hadarin a iya maida su sojoji.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta ce ta sami rahotanin da suka nuna cewa ana kashe fararen hula a barin wuta ko kuma baruguzan gidaje su binne su.

Akwai kuma rahotannin da suka nuna cewa ‘yan ISIS na amfani da Daruruwan iyalai wajen yin garkuwa da su, a cewar mai magana da yawun hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijirar William Spindler.

Wasu iyalai su 625 sun sami sa'ar kubuta da ficewa daga wannan fadan cikin makon da ya gabata.

Related

  • Ranar Fadakarwa Kan Illar Taba Sigari

  • A Amurka Jiya Litinin Ce Ranar Tunawa da Wadanda Suka Sadakar da Rayukansu

  • Israila Ta Nada Wani Mai Tsananin Ra'ayin Rikau Ministan Tsaro

  • Tsagerun Niger Delta Na Kara Kai Hare-hare

  • Gwamnatin Buhari Ta Dakatar da Bayyana Sunayen Wadanda Suka Wawure Dukiyar Kasa

  • 'Yan Rajin Kafa Kasar Biafra Sun Yi Kazamar Zanga-zanga

  • Nijar Bata Morar Zafin Rana Wajen Samun Makamashi

You might like also

  • Sauran Duniya

    An Harbe Wata Mawakiya Har Lahira a Amurka

  • Afirka

    Al Shabab Ta Kashe Mayakanta

  • Najeriya

    Kocin Najeria Shu'aibu Amodu Ya Rasu

  • Najeriya

    An Yiwa Manyan Sojojin Najeriya Ritaya

  • Najeriya

    Najeriya: Magidanta Na Korafi Kan Tsadar Kayan Masarufi

  • Sauran Duniya

    Bom Ya Tashi Cikin Masallaci Lokacin Da Ake Sallar Juma'ar Yau

Show comments

Back to top
XS
SM
MD
LG