This version of the page http://www.voahausa.com/a/3315284.html (0.0.0.0) stored by archive.org.ua. It represents a snapshot of the page as of 2016-06-04. The original page over time could change.
Afrika Zata Gudanarda Taron Kan Shirin Dashen Itatuwa

Accessibility links

  • Koma Ga Cikakken Labari
  • Koma Ga Babbar Kofa
  • Koma Ga Bincike
Harsuna
Afirka

Afrika Zata Gudanarda Taron Kan Shirin Dashen Itatuwa

  • Abubakar Jinaidu

  • Nuna wa mutane akan Facebook
  • Nuna wa mutane akan Twitter
  • Nuna wa mutane akan Google+
  • Tura Ga Aboki ta Email

Tun shekarar 2005 aka fidda shawarar shirin da ake kira da turanci "Great Green Wall"

A wannan makon ne Kungiyar Kasashen tarayyar Afrika zata gudanarda taron farko na kasa-da-kasa kan shirin dasa itattuwa a birnin dakar na kasar Senegal. Babban burin wannan shirin dai shine fito matakan kawas da kwararowar hamada a yankin kasashen da ke yamma da hamada, abinda kwararru suka ce yana kawo talauci da rashin tsaro.

A babban taron kolin sauyin yanayi na kasashen duniya da aka yi a birnin Paris a watan Disambar bara, shugabannin kasashe sun dauki alkawarin bada taimakon dala biliyan 4 nan da shekaru 5 don farfado da yankin na Afrika. A kan haka ne yanzu wakilai daga kasashe 20 daga yankunan arewa da yammacin sahara suke ganawa da kwararru da kungiyoyi a Dakar don tattanawa akan yadda za a fitowa lamarin.

Tun shekarar 2005 aka fidda shawarar shirin da ake kira da turanci "Great Green Wall", wanda kuma tsohon shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade ya bada jagorancin karfafa shi.

Kudirin shine a dasa dubban itatuwa masu yawa da zai shafi yanki mai nisan dubban kilometoci daga Senegal zuwa Djibouti don magance kwararar hamada daga yankunan dake kudu da hamada.

Related

  • Trump ne ke kan gaba a jihar Indiana a zaben fidda gwani na Republican

  • 'Yan Shi'a sun janye zanga zangarsu a Bagdaza

  • 'Yan adawan Venezuela na cigaba da kokarin tsige shugaban kasar

  • Amurka da Rasha su daidaita lamura tsakaninsu a yankin Baltics -Admiral Richardson

  • Jami'an Kenya sun kama mai ginin da ya rushe ya hallaka mutane

  • Direbobin tankokin dakon man fetur na barazanar shiga yajin aiki

  • A jam'iyyar PDP wasu tsoffin ministoci biyu sun kaure da cacar baki

You might like also

  • Shirin Rana

    Shirin Rana

  • Shirin Hantsi

    Shirin Hantsi

  • Shirin Safe

    Shirin Safe

  • Shirin Dare

    Shirin Dare

  • Yau da Gobe

    Yau da Gobe

  • Shirin Rana

    Shirin Rana

Back to top
XS
SM
MD
LG