Alhamis, Afrilu 28, 2016 Karfe 06:52
Cikin Sauti
Rumbun Kallo
YouTube
Rumbun Hotuna
Shigo Mu Tattauna A Dandalin Tamaula

    Labarai / Najeriya

    An Bude Cibiyar Kula Da Masu Fama Da Cutar Gubar Dalma

    An koyarda likitocin jihar Neja yadda zasu yi saurin gano wadanda suka harbu da cutar ta gubar dalma.

    I

    Labarai Masu Alaka

    • Shaguna Sama Da Dubu Ne Suka Kone Kurmus Sakamakon Gobara A Kano
    • Sarakuna Suna Da Tasiri Wajen Inganta Tsaro A Kasa.
    • Shugabannin Addinin Kirista A Najeriya Sunyi Kira da A nuna Tausayi Ga Juna.
    • Kungiyar Maharba Ta kasa Da Kasa Tayi Taro
    • Masu Karban Kudin Fansho A Jihar Bauchi Sun Koka.
    • An Kame Wata Yarinya ‘Yar kunar Bakin Wake Wadda Tace Tana Cikin Yan Matan Chibok.
    • Babbar Kasuwar Bernin Kebbi Ta Kone Kurmus.
    Abubakar Jinaidu

    Kungiyar likitoci na kasa da kasa tare da Gwamnatin jihar Neja, sun bude cibiyar kula da masu fama da cutar gubar dalma dake hallaka jama’a a jihar ta Neja.

    Jihar Neja, na daya daga cikin jihonin da ake samun masu ginar ma’adanai na karkashin kasa ba’a kan ka’ida ba alamarin da kwararru akan fanin suka ce yana hadasa bazuwar cutar ta gubar dalma.

    An dai bude cibiyar ne a yankin  karamar hukumar Rafi, inda aka sami barkewar cutar gubar dalma da ta hallaka yara ashirin da takwas tare da dabbobi sama da dari a shekarar bara.

    Kwamishnar lafiya na jihar Neja, Dr, Mustapha Jibril, yace hakarma’adinai da ake yi ba’a bisa ka’ida ba shine sanadiyar barkewar cutar gubar dalma wanda ke gurbata ruwa.

    Ya kuma kara da cewa kungiyar agajin likitoci ta duniya wato “ Doctors without Boarders” suma sun kawo dauki.

    A karkashin wanan shirin likitocin kasa da kasar har sun koyarda likitocin jihar Neja, akan yadda za’a yi saurin gano wadanda suka harbu da cutar ta gubar dalma.

     

    An Bude Cibiyar Kula Da Masu Fama Da Cutar Gubar Dalma - 3'00"
    An Bude Cibiyar Kula Da Masu Fama Da Cutar Gubar Dalma - 3'00"i
    ▶ || 0:00:00
    ... ⇱  
    • MP3 - 2.8MB
    • none - 8.3MB
    • MP3 - 706.3kB
     
     
    X

     

    Watakila Za A So…

    Ba tare da bata lokaci zan canza manufofin harkokin wajen Amurka - Donald Trump

    Dan takarar nema shugabancin Amurka na sahun gaba a karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump, a jiya Laraba yace, ba tare da bata lokaci ba zai canza harkokin diflomasiyyar Amurka in ya ci zabe. Karin Bayani

    Ted Cruz na jam'iyyar Republican ya zabi Fiorina a matsayin mataimakiyarsa

    Daya daga cikin masu neman jam’iyyar Republican ta tsayar da shi dan takararta na neman shugabancin Amurka Ted Cruz, ya zabo tsohuwar jami’ar wani kamfanin na’ura mai kwakwalwa kuma tsohuwar ‘yar takara Carly Fiorina a matsayin mataimakiyar Shugaban Kasa in yaci zabe. Karin Bayani

    Amurka na tuhumar wasu mutane da suka ki jinin 'yan Somalia uku

    Masu gabatar da kara na Amurka sun sanar da tuhumar wasu mutane biyu bisa aikata laifukan tsana ko nuna kin jinin wasu mutanen Somalia guda 3 da suka farwa a birnin Dodge dake jihar Kansas a watan Yunin bara. Karin Bayani

    Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'ar girka sojoji a yammacin Sahara

    Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya shirya kada kuri’a ranar Juma’a mai zuwa game da bukatar Amurka na farfado da ajiye dakarun kiyaye zaman lafiya a Yammacin Sahara, bayan Morocco ta kori ma’aikatan MDD 83 a watan da ya wuce. Karin Bayani

    Hukumar zaben Kenya zata gyara kurakuran zaben shekarar 2013 kafin zaben badi

    Wani kusa daga Hukumar Zaben Kasar Kenya mai zaman kanta da kuma Hukumar Kula da kan iyakoki yace, hukumar zaben tana son inganta ayyukanta ta hanyar la’akari da zaben shekarar 2013, saboda shirye-shiryen zaben kasar da za a yi a badi. Karin Bayani

    Rundunar sojin Najeriya ta bankado wata makarkashiya da kungiyar Boko Haram ke yi

    Sojojin Najeriya sun ce sun bankado wata makarkashi da 'yan Boko Haram ke anfani da ita wajen yaki da al'ummar Najeriya Karin Bayani

    An rufe wannan dandalin
    Sharhi/Ra'ayi
         
    Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

    Wasu Labarai na wannan Marubuci

    • Ana Sa Ran Teodoro Obiang Ne Zai Lashe Zaben Equatorial Guinea Don Sake Wani Wa’adin Shugabanci
    • Donald Trump Yanzu Yana Da Wakilai 950 Cikin 1237
    • Kungiyar Taliba Na Sa Ran Samu Maslaha
    •  Gwamnatin Yanzu Da Na Baya Akwai Banbanci
    •  An Sasanta Fada Ya Kare A Taraba Da Adamawa
    Karin Labarai

    Sauti

    • Minti 30

      Shirin Safe

      Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

    • Minti 30

      Shirin Dare

      A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

    • Minti 30

      Yau da Gobe

      Yau da Gobe

    • Minti 30

      Shirin Rana

      Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

    • Minti 30

      Shirin Hantsi

      Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

    • 1
    • 2
    • 3
    • 4
    • 5
    Karin Bayani akan Shirya-shirye
    Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
    Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
     
    Karin Bayani akan Shirya-shirye